BBC navigation

Gyaran tsarin mulki:'Yan Majalisar wakilan Najeriya zasu soma tuntubar mazabun su

An sabunta: 8 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:51 GMT
Najeriya

An soma yunkurin gyaran tsarin mulki

A Najeriya, majalisar wakilan kasar ta kaddamar da shirinta na tura mambobinta zuwa mazabunsu domin su tattara ra'ayoyin al'uma dangane da yunkurin da majalisar ke yi na yin gyara ga kundin tsarin mulkin kasar.

Majalisar dai ta ci alwashin fifita ra'ayin jama'a a dukkan gyaran-fuskar da za ta yi.

'Yan kasar da dama dai na ci gaba da gabatar da bukatu da daban-daban, ciki har da neman kirkirar sababbin jihohi.

Wasu batutuwa kuma da za a ji ra'ayoyin jama'a dangane da su, sun hada da batutuwan da suka shafi hakkin zama dan kasa, da kirkiro kananan hukumomi da dai sauransu

Kungiyar kwadagon Najeriya dai tace zata sa ido sosai don tabbatar da cewar an yi amfani da ra'ayoyin jama'ar da aka tattaro.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.