BBC navigation

Obama ya koma Fadar White House bayan zabe

An sabunta: 8 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:40 GMT

Shugaba Obama

Shugaba Obama ya koma fadarsa ta White House kwana guda bayan nasararsa a wa'adin mulki na biyu.

Tuni dai shugaba Obama ya kira shugabannin majalisar dokokin kasar inda ya bukace su da su yi kokarin shawo kan matsalar gibin kasafin kudin kasar tare.

Sabon zababben shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan kasar John Boehner ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da 'yan jam'iyyar Democrats don warware matsalar cikin gaggawa, amma ya hakikance kan aiwatar da manufofi masu daukar dogon lokaci.

Ya ce, "shugaban kasa, 'yan Jamiyyar Republican masu rinjaye a majalisar wakilai a shirye muke mu yi aiki tare da kai, don yiwa kasar nan abinda ya dace."

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.