BBC navigation

Farashin Kayan masarufi ya tashi a China

An sabunta: 9 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:10 GMT

Hu Jintao

Tashin farashin kayan masarufi a kasar China ya yi matukar raguwar da ba a ga irinta ba a cikin shekaru uku da suka gabata.

Kididdigar hukuma ta nuna cewa farashin kayayyakin da mutanen kasar ke amfani da su ya tashi da kashi daya da digo bakwai cikin dari a tsakanin watan Octoban bara zuwa Octoban bana.

Bayan shekara da shekaru ana bayyana damuwa game da hanyar da za a bi wurin shawo kan matsalar tashin farashin kaya a kasar, gwamnatin Chinan a bara ta mayar da hankali kan kokarin rage yadda farashin ke tashin gwauron zabi.

Wannan na zuwa ne a lokacin da Jam'iyyar Kwaminis ke babban taron ta wanda daga karshe zai bayyana sabbabin shugabanni a kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.