BBC navigation

Yadda ake mulkin China

An sabunta: 12 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:47 GMT
CLICKABLE
Jam'iyyar Kwaminis

Tsayawa bayyana yadda ake tafiyar da gwamnatin China ba abu ne mai sauki ba, kasancewar sau da yawa abin da ke rubuce kan saba da abin da ake aikatawa a zahiri.

Kundin tsarin mulkin kasar ya tanadi cewa majalisar dokoki ce ke da magana ta karshe a kan al'amura. Amma a zahiri wadansu 'yan tsirarun mutane su tara (wani lokaci su bakwai)--wadanda ake kira Kwamitin Dindindin na Majalisar Gudanarwa--su ke da wuka da nama.

Wadannan mutane masu fada-a-ji suna raba mukaman jam'iyya da na gwamnati a tsakaninsu; hakan ya sa za a samu mutum daya yana rike da mukamai biyu zuwa uku, amma aikin jam'iyya shi ne kan gaba.

Misali, jagoran kasar, Hu Jintao, shi ne shugaban kasa, mukamin da na je-ka-na-yi-ka ne idan aka kwatanta da sauran mukamansa guda biyu--mukamin Babban Sakataren jam'iyya, da kuma mukamin Shugaban Hukumar Kula da Al'amuran Sojin kasar.

Shi kuwa mutum na uku mafi girman mukami a kasar, Wen Jiabao, yana rike ne da mukamin Firayim Minista. Sauran abokan aikinsa su ke kula da kotuna, da 'yan sanda da kuma harkar farfaganda.

A takaice dai wadannan mutane 'yan tsiraru su ne ke mulkin kasar mai yawan al'umma biliyan daya da miliyan dari uku.

Ba kasafai suke bayyana tare a bainar jama'a ba, amma idan hakan ta kasance to zai zama babban labari ga kafofin yada labaran kasar. Mutanen tara sun bayyana ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 2012 a Dandalin Tiananmen, wurin da aka murkushe zanga-zangar dalibai ta neman tattabar da tsarin dimokuradiyya, inda suka ajiye furanni a gindin Hasumiyar Tunawa da Jaruman Kasa a matsayin wani bangare na bikin cikar Jamhuriyar Kasar China shekaru sittin da uku da kafuwa.

Sai dai ga bakwai daga cikinsu, wannan ce fitowa ta karshe a bainar jama'a, domin za a maye gurbin su da wadansu sababbin shugabanni wadanda za su mulki kasar--wacce ita ce ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya--a shekaru goma masu zuwa. Za a yi sauyin shugabancin ne yayin Babban Taro na kasa da jam'iyyar za ta gudanar a Beijing.

Kamar kullum, gwagwarmayar neman mulki a tsakanin bangarori da ma daidaikun mutane a jam'iyyar na cikin abubuwan da ke gudana yayin sauyin na shugabanci.

Kuma a wannan karon, gwagwarmayar ta fi tsanani bayan faduwar bakar tasar da sanannen dan siyar nan Bo Xilai--wanda daya ne daga cikin fitattun masu neman kujera a Kwamitin Dindindin na Majalisar Gudanarwa kuma tsohon shugaban jam'iyyar a birnin Chongqing mai mutane miliyan goma sha daya--ya yi.

Da yake bayar da sanarwar korar Bo Xilai daga jam'iyyar, kamfanin dillancin labarai na gwamnati, wato Xinhua, ya jero laifuffuka da dama da ake tuhumarsa da aikatawa da suka sabawa dokokin jam'iyya.

Hukumomin kasar China suna so su yi amfani da wannan dama don nuna cewa da gaske suke yi a yunkurinsu na yakar cin hanci da rashawa. Amma da wahala su gamsar da al'umar kasar wadanda ke kara nuna shakku da yunkurin gwamnatin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.