BBC navigation

'China za ta sha gaban Amurka a karfin tattalin arziki'

An sabunta: 9 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:10 GMT
China

China zata sha gaban Amurka ta fuskar tattalin arziki

Daya daga cikin fitattun cibiyoyin tattalin arziki, wato OECD ta yi hasashen cewa, za'a samu wani gagarumin sauyi a duniya dangane da karfin arziki tsakanin kasashe nan da shekaru hamsin.

Wani sabon rahoton kungiyar ta OECD yace, nan da shekara ta 2016 China zata shiga gaban Amurka ta fuskar karfin tattalin arziki.

Kuma nan da kasa da shekaru hamsin, tattalin arzikin kasashen China da India jimulla zai zarta na dukkanin kasashen da suka cigaba.

Kungiyar ta OEDC ta kuma ce, kasashen da tattalin arzikinsu yake bunkasa zasu shiga gaba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.