BBC navigation

An dau matakin ladabtar da dakarun Amurka

An sabunta: 9 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:18 GMT

Sojin ruwa na Amurka

An dauki matakin ladabtar da dakarun Amurka na musamman guda bakwai.

A cikin wadanda za a ladabtar din har da daya daga cikin wadanda suka kai harin da ya yi sanadiyyar rasuwar Osama bin Laden, saboda zarginsu da bayyana wasu bayanan sirri.

Sun bayar da bayanan sirrin ne dai a lokacin da aka dauke su a matsayin masu bayar da shawarwari wurin shirya wani wasan bidiyo wanda ke nuna yadda sojoji ke kai samame.

An kuma tuhumi sojojin guda bakwai da yin sakaci da aikinsu da kuma rashin biyayya ga umarni.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.