BBC navigation

Dole ne attajiran Amurka su biya haraji mai yawa in ji Shugaba Obama

An sabunta: 9 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:34 GMT
Shugaba Obama na Amurka

Attajiran Amurka zasu soman biya haraji mai yawa

Shugaba Obama na Amurka yace, dole ne attajiran Amurka su biya haraji mai yawa domin shawo kan matsalar gibin kasafin kudi da kasar ke fuskanta.

Yayin da yake share fage kafin tattaunawa da majalisar dokoki domin kaucewa rikici akan kasafin kudi, shugaba Obama yace, a shirye yake a fahimci juna da 'yan jam'iyyar Republican.

Sai dai kuma Obama yace, ba zai amince da duk wani tsari ba, da ba zai daidaita tsuke bakin aljihun gwamnati da karawa attajirai haraji ba.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.