BBC navigation

Obama ya ce dole attajirai su biya haraji mai tsoka

An sabunta: 10 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:08 GMT

Shugaba Barack Obama

Shugaba Obama na Amurka ya ce, dole ne attajiran Amurka su biya haraji mai yawa domin shawo kan matsalar gibin kasafin kudi da kasar ke fuskanta.

Yayin da yake share fage kafin tattaunawa da majalisar dokoki domin kaucewa rikici akan kasafin kudi, shugaba Obama ya ce, a shirye yake ya fahimci juna da 'yan Jam'iyyar Republican.

Sai dai kuma Obama yace, ba zai amince ba da duk wani tsari, da ba zai daidaita tsuke bakin aljihun gwamnati da karawa attajirai haraji ba.

A nata bangaren, Jamiyyar Republican wadda ke da rinjaye a majalisar wakilan kasar, na matukar adawa da karin haraji.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.