BBC navigation

Akalla Mutane 27 sun mutu a gidan-yarin Sri Lanka

An sabunta: 10 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:46 GMT

Gidan-yarin Sri Lanka

Hukumomin Gidan-yarin kasar Sri-Lanka sun ce a kalla mutane ashirin da bakwai sun halaka sakamakon wani mummunan tashin hankali da ya afku a Gidan-yarin kasar da aka yi shekara da shekaru ba a ga irinsa ba.

Mahukuntan sun ce yawancin wadanda suka rasu a Gidan-yarin na Welikada dake Colombo fursunoni ne.

Sai dai daga cikin sauran mutanen da suka jikkata, har da jamian tsaro.

Wakilin BBC ya ce Daraktan asibitin da aka kai gawarwakin da suka rasun, ya ce mutane arba'in da uku ne suka jikkata, cikinsu har da fursunoni da jami'an 'yan sanda da sojoji guda hudu da kuma mai gadin gidan yarin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.