BBC navigation

'Yan adawar Syria sun soma tattaunawa a Qatar

An sabunta: 10 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:20 GMT
'Yan adawar Syria

'Yan adawar Syria su na tattaunawa

An soma wata tattaunawa a Qatar tsakanin kungiyoyin 'yan adawa a Syria akan samar da wani shugabanci guda

Tattaunawar ta hada da manyan kungiyoyin 'yan adawa dake wajen Syria da kuma wakilan kungiyoyin mayakan 'yan tawaye dake fada a cikin Syrian kan ta

Kungiyar abokanan Syria dake samun goyan bayan Amurkawa na fatan ganin an samu wata kungiyar 'yan adawa guda wacce zata taka rawa tamkar gwamnatin dake jiran gado

Sabon zababben shugaban Kwamitin 'yan adawa na Syria ya fadawa BBC cewa ba lallai bane tattaunawar ta haifar da wani sakamako nan take

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.