BBC navigation

Tilas BBC ta maido da martabarta

An sabunta: 11 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:14 GMT
Lord Patten

Shugaban hukumar gudanarwa ta BBC

Shugaban hukumar gudanarwa ta BBC, Lord Patten ya bayyana cewa kafar yada labarai ta BBC na bukatar wani gagarumin garambawul na ba sani ba sabo na shugabanninta.

Wannan ya biyo bayan murabus din da babban daraktan BBCn George Entwhistle ya yi a jiya, akan wani rahoto da aka watsa game da cin zarafi yara.

Lord Patten ya ce kima da martabar kafar yada labarai ta BBC zata zube muddin ya kasance ba yadda tsakaninta da masu sauraranta.

Da yake magana a gidan talabijin na BBCn Mr Patten ya ce ba ya tsammanin abunda mutanan burtaniya ke so ba kenan.

Amma dai ya yi ammanar cewa BBC na bukatar yin wani gagarumin garabawul na ba sa ni ba sabo domin ta fidda kanta daga cikin wannan rikici da ya dabaibayeta.

Har ila yau Lord Patten ya musanta maganganun da ake na cewa an tilastawa shugaban BBCn, Goerge Entwhistle yin murabus ne.

Inda ya ce ya ta fi ne da martabarsa wanda hakan ne mafi a'ala a gare shi.

Wata kusa a gwamnatin Burtaniya kuma, Theresa May ta ce yanzu abinda BBC zata fi mai da hankali a kai shi ne tilas ta dauki matakan maido da amincin da ke tsakaninta da jama'a da kuma martabarta ta aikin yada labarai.

Jama'a da dama a ciki da wajan BBCn sun yi ammanr cewa kafar yada labaran na cikin tsaka mai wuya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.