BBC navigation

ECOWAS za ta dauki matakin soji a Mali

An sabunta: 11 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:23 GMT
Taron shugabannin ECOWAS a kan Mali

Taron shugabannin ECOWAS a kan Mali

Taron shugabanin kungiyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ,wato ECOWAS ko kuma CEDEAO ya amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa , dubu uku da dari uku zuwa kasar Mali domin samar da zaman lafiya.

Sai kungiyar ta ce har yanzu ba ta rufe kofa ba game da tattaunawar sulhu.

Kungiyar ta ce ba za ta zura ido har sai lamura sun gama dagulewa a kasar Mali ba .

Wannan ne ya sa shugabanin kungiyar su ka yanke shawarar tura dakaru don daidaita alamura a kasar.

Alasan Ouatara shugaban kasar COTE D'IVOIRE ,shi ne shugaban kungiyar ta Ecowas ko kuma CEDEAO ya yiwa manema labarai bayani kan shawarar da kungiyar ta dauka.

Sai dai bai fadi takamaimai lokacin da za su tura dakarun ba, sabo da a cewar sa ,sai sun turawa kungiyar tarrayra Afrika shawarar ta su, ita kuma ta turawa majalisar dinkin duniya kafin tura dakarun.

Har wa yau kungiyar ta ECOWAS ta ce za ta ci gaba da duba hanyoyin sulhu na shawo kan rikicin kasar ta Mali,sai dai ba ta fayyace yadda za ta tamna taura biyu a baka ba, wato hada amfani da karfin soji da kuma sulhu a lokaci guda ba.

A game da maganar kasar Guinea Bissau ,wasu matakai da taron ya dauka sun hada da kiran taron tattaunawa a majalisar dokokin kasar ,da sake jaddada wa'adin zaman dakarun majalisar dinkin duniya a kasa da wata 6 nan gaba, gani wadin zai kare a ranar 17 ga wanan wata, sun yin allawadai da kokarin juyin mulkin da aka yin yunkurin yi a ranar 21 ga watan Aprilu a kasar.

Kazalika kungiyar ta yi, kira ga kungiyar tarrayar Afrika da ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar ta Guinea Bissau, domin su bawa hukumomin rukon kwarya na kasar kwarin gwiwa,su kuma samu sukunin shirya zaben shugaban kasar a cikin watan aprilu na shekara 2013.

Kimanin watanni 8 kenan kasar Mali ke fama da rigingimu ,inda bangaren arewacin kasar ya fada hannun yan tawaye.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.