BBC navigation

Daraktan BBC Entwistle ya sauka daga mukaminsa

An sabunta: 11 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 04:29 GMT

George Entwistle

Babban Daraktan BBC, George Entwistle wanda ya hau shugabanci a watan Satumba ya sauka daga mukaminsa.

Mista Entwistle ya sauka ne a lokacin da BBC ta yi wani rahoto a wani shirin ta na Newsnight Talabijin din da ake gani a Birtaniya inda aka yi kuskuren bayyana wani tsohon dan siyasa a matsayin mai lalata da kananan yara.

Bisa kallon da akewa BBC na yin taka tsan-tsan da binciken tsohon ma'aikacinta Jimmy Savile da kuma saurin bayyana tsohon jigo a Jamiyyar masu ra'ayin rikau kan lalata da kananan yara,, George Entwistle ya ga ba shi da wani zabi illa ya sauka daga mikaminsa.

Tun farko dai Entwistle ya ce rahoton da BBC ta cikin gida ta yi wanda ya zayyana babban jigo na siyasar kasar Tory Lord McAlpine bai kamata ma a watsa shi ba.

A sanarwar da ya bayar, Entwistle ya ce don gane da cewa Director Genaral shine kuma babban Edita sannan kuma shine yake da alhakkin duk wani shiri da aka watsa da kuma abin da ya faru ba na lamunta ba ne (wato kan shirin da Newsnight suka yi ranar Jumaa biyu ga watan Nuwamba,) abin da yafi shine ya bar mikamin Director General din.

George Entwistle dai yana kan mikamin ne aka zargi BBC da yin rufa rufa kan zargin da ake yi wa tsohon ma'aikacinta Jimmy Savile da yin lalata da 'yan mata.

Shugaban BBC Trsut Lord Pattern wanda yayi jawabi bayan da Entwistle ya yi murabus ya ce wannan yammaci ne mai cike da damuwa a cikin rayuwarsa.

Ya kara da cewa George ya bar aiki ne saboda kuskuren da ba za a lamunta ba wanda ya saka BBC cikin rudani.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.