BBC navigation

Isra'ila ta ja kunnan gwamnatin Syria

An sabunta: 11 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 18:42 GMT
Sojojin Isra'ila a yankin Golan

Sojojin Isra'ila a yankin Golan

Isra'ila ta ce ta harba makami mai linzami cikin Syria, bayan da aka harba wani makamin roka wajan da dakarunta suke a tuddan Golan, wanda ta yi ammanar dakarun gwamnatin Syrian dake fada da 'yan tawaye ne suka harba shi.


Wannan dai na zuwa a a dai dai lokacin da dakarun 'yan adawa na Syrian dake taro a Qatar suka bada sanarwar cewa, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar kafa wata kungiya daya da zata samar da gwamnatin rikon kwaryar, ta kuma zama a kan gaba wajan bada tallafi a wuraran da ke hanun 'yan tawayen na Syria.

Wannan shi ne karan farko da Isra'ila ta harba makami akan Syria tun bayan yakin da aka gwabza a shekarar 1973 a yankin gabas ta tsakiya.

Sojojin Isra'ila sun ce an harba makamin mai linzami daya cikin Syria, bayan da wani makamin roka ya fada a wajan dakarun Isra'ila dake yankin tuddan Golan, amma bai taba kowa ba.

Avital Leibovich mai magana da yawun sojojin Isra'ila ta ce sun gano cewa abun da ya faru sakamakon rikicin da ake ne a cikin Syria ba wai an harbo kan Isra'ila ba ne.

Isra'ila kuma ta harba makamai na gargadi a wasu wuraran a Syria kuma ta mika koken ta ga majalisar dinkin duniya akan wannan lamari.

Wannan dai shi ne irinsa na baya bayannan kuma Isra'ila ta fito karara ta ce zata mai da martani muddin hakan ya da da faruwa.

A fili ta ce cewa wannan na da nasaba da fadan da dakarun Syria ke gwabzawa da 'yan tawaye.

A waje daya kuma 'yan adawar da suka kwashe mako guda suna tattaunawa a Doha babban birnin Qatar, sun ce sun cimma yarjejeniyakan kafa wata kungiyar hadin guiwa, wadda zata kunshi dukkan manyan kungiyoyin 'yan adawar dake ciki da wajan Syria.

Kasashen yammaci sun ce za su amince da kungiyar tare da mara mata baya.

Nan gaba ne ake saran za su yi karin haske ga me da wannan yarjejeniya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.