BBC navigation

An yankewa tsohon babban jami'in leken asirin Jordan hukuncin daurin shekaru 13

An sabunta: 11 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:19 GMT
Sarki Abdallah na Jordan

An daure tsohon babban jam'in leken asirin Jordan

An yankewa wani tsohon babban jami'in leken asirin Kasar Jordan Janar Mohammad al Dahabi hukuncin daurin shekaru 13 a gidan yari, saboda samun sa da laifin almundahana da kudaden jama'a da kuma amfani da mukaminsa ba ta hanyar da ya dace ba

Wannan ita ce shari'a mafi girma da aka gudanar tun lokacin da Sarki Abdallah ya kaddamar da yaki da cin hanci, bayan da 'yan Kasar suka gudanar da wata zanga zanga inda suke neman a gudanar da sauye sauye a tsarin siyasar Kasar

An tsare tsohon baban jami'in leken asirin ne a watan Fabrairu, bayan da jami'an babban bankin kasar su ka gano cewar wasu miliyoyin daloli da suke da shakku akai, sun shiga cikin asusun sa na banki

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.