BBC navigation

'Yan fashi a Kenya sun harbe 'yan sanda 7

An sabunta: 11 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:05 GMT

Shanu a Kasar Kenya

Wasu 'yan fashin shanu a kasar Kenya sun harbe 'yan sanda a kalla bakwai har lahira tare da jikkata wasu da dama.

Wani kakakin 'yan sandan a yankin Rift Valley ya ce maharan samame suka kai wa 'yan sandan a lokacin da suke kokarin kwato wasu daruruwan shanu da aka sace a yankin Samburu dake tsakiyar kasar ta Kenya.

Wakilin BBC ya ce kashe-kashen da 'yan fashin shanu ke yi, ba sabon abu ba ne, amma mummunaN hari irin wannan kan 'yan sanda, abu ne da ba a saba gani ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.