BBC navigation

An kashe Palasdinawa biyar a Zirin Gaza

An sabunta: 11 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:13 GMT

Hari a Zirin Gaza

Palasdinawa guda biyar ne aka kashe sannan kimanin ashirin suka jikkata sakamakon wani dauki ba dadi da suka yi da Israela a iyakar Israela da zirin Gaza.

Palasdinawa ta Islamic Jihad ta ce Israela ta kashe dan kungiyar guda daya sakamakon wani hari ta sama.

A matsayin martani na harin igwa da Israela ta kai yankin Palasdinawa wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane hudu, an yi ta ruwan harin rokoki da bama bamai a kudancin Israela.

Wasu kafofin watsa labaran Palasdinawa sun nuna cewa, dukkanin wadanda aka kashe fararen hula ne.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.