BBC navigation

An kashe 'yan sanda 42 a Kenya

An sabunta: 12 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:34 GMT

Rahotanni daga Kenya sun ce yawan 'yan sandan da aka kashe a wani kwanton bauna da barayin shanu su ka yi masu a ranar Asabar yanzu ya kai 42.

Wadanda su ka shaida al'amarin da kuma majiyoyin 'yan sanda sun ce an gano wasu karin gawawwakin 'yan sanda a yau a lardin Samburu na arewacin kasar, inda aka kai harin.

Sai dai ministan tsaron cikin gidan Kenya, Katoo ole Metito, ya ce gwamnati na lura sosai da al'amurra.

Ya ce: "Wannan wani abun bakin ciki ne da ba kasafai yake faruwa ba. Amma gwamnati ta na sa ido a kan komai a yankin".

Mazauna yankin dai sun ce su na fargabar za'a samu karin tashin hankali yayinda ake zaman zullumi a sakamakon sintirin da jami'an tsaro ke yi a kauyuka.

Kakakin 'yan sanda, Eric Kiraithe, ya ce an kashe ukku daga cikin wadanda su ka kai harin, yayinda tara daga cikin jami'an tsaron da aka jima raunuka ke can kwance a asibiti.

Kafafen yada labarai na Kenyan sun ce wani irin wannan harin da aka kai makonni biyu da suka wuce ya jawo halakar mutane 12 a kusa da wajen.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.