BBC navigation

Messi ya zarta Pele a tarihin cin kwallo

An sabunta: 12 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 11:32 GMT

Lionel Messi

Dan wasan Barcelona, Lionel Messi, ya kafa sabon tarihi a fagen kwallon kafa inda ya zarta tsohon dan kwallon Brazil Pele, wanda ya zura kwallaye 75 a shekara daya.

Kafin wannan lokaci, Pele ne na biyu a tarihin zura kwallaye masu yawa cikin shekara guda, inda yake bayan Gerd Muller, wanda ya ci kwallaye 85 a wasanni 60 lokacin da yake kulob din Bayern Munich da Jamus ta Yamma a shekarar 1972.

Sai dai a yanzu Messi, dan shekaru 25, shi ne ke bin bayan Muller, bayan da ya zura kwallaye biyu a wasan da kulob din sa ya buga da Mallorca ranar Lahadi.

Don haka yanzu ya zura kwallaye 76 a wasanni 59 da ya buga.

Hakan dai ya sanya shi a hanyar lashe kyautar Ballon d'Or a karo na hudu a jere.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.