BBC navigation

Za'a ba da belin Abu Qatada

An sabunta: 12 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 21:16 GMT

Za'a ba da belin malamin nan mai kaifin ra'ayin Islama, Abu Qatada, bayan da ya yi nasara a daukaka karar da ya yi kan yunkurin da hukumomin Burtaniya ke yi na tesa keyarsa zuwa Jordan inda ake zarginsa da shirya kai hare-haren bam.

An shirya a gobe ne za'a sake shi, amma zai zauna a cikin gidansa ne na tsawon sa'o'i 16 a rana.

Wata hukumar kula da daukaka kararrakin da suka shafi shige-da-fice ta ce ba ta gamsu da tabbacin da gwamnatin Burtaniya ta bayar ba cewa ba za'a yi amfani da bayanan da aka tatsa daga Abu Qatada ta hanyar azabtar da shi ba a shari'ar da za'a yi ma shi a Jordan.

Sakatariyar harkokin cikin gida ta Burtaniya, Theresa May, ta ce Abu Qatada mutum ne mai barazana ga tsaron lafiya, kuma ana zargin sa da ta'addanci.

Kafin hukumar da yanke hukunci dai lauyan Abu Qatadan, Edward Fitzgerald, ya gaya mata cewa babu wata hujjar ci gaba da tsare Abu Qatadan.

Ya ce: "Ya isa haka nan; an tsare shi shekara da shekaru".

Abu Qatada, wanda sunansa na ainihi shine Omar Othman, ya na fuskantar shari'a a Jordan kan zargin hada-baki don kai hare-hare ga wasu 'yan kasashen Yammacin duniya da Isra'ila a shekarar 1998 da kuma shekarar 1999.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.