BBC navigation

Yau Litinin ce ranar cutar Pnuemonia ta duniya

An sabunta: 12 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 08:41 GMT

Wata Jami'ar Hukumar Lafiya ta Duniya tana baiwa wani yaro maganin cutar shan inna a birni Mogadishu na kasar Somaliya.

Yau ce ranar da aka kebe don fadakar da al'uma a kan cutar sanyin huhu wato pneumonia, cutar da masana ke cewa na halaka kananan yara 'yan kasa da shekara biyar da haihuwa.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce cutar na daga cikin muggan cututtakan da ke yi wa yara illa a duniya, kasancewar tana halaka sama da yara miliyan daya da dubu dari biyu a kowace shekara.

Kazalika mafi yawan yaran da ake haihuwa na mutuwa ne saboda karancin magungunan da ke kara musu karfin garkuwar jiki.

Najeriya dai na daga cikin kasashenda aka fi fama da wannan cuta ta Pneumonia a duniya,inda alkaluman da mahukuntan kasar suka fitar ke nuna cewa sama da kananan yara 160,000 ne ke mutuwa a kowace shekara sakamakon kamuwa da cutar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.