BBC navigation

Takaddama a kan tono gawar Yasser Arafat

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:31 GMT
Marigayi Yasser Arafat

Tsohon jagoran Palasdinawa

An killace kabarin tsohon shugaban Hukumar mulkin Palesdinawa, Yasser Arafat a yunkurin da ake yi na tantance zargin da ake yi cewa an kashe shi ta hanyar ba shi guba.

An bunne gawar Mr Arafat ne a birnin Ramallah na Gabar Yammacin Kogin Jordan, bayan ya rasu a wani asibitin Faransa a shekara ta 2004, amma ba'a bayyana musababbin mutuwarsa ba.


Wakilin BBC ya ce har yanzu dai ba'a tsaida ranar da za'a tono gawar Mr Arafat din ba, amma jami'an Palasdinawa sun yi imanin cewa za'a yi hakan a cikin 'yan makonni masu zuwa.


A cikin watan Agusta ne Faransa ta kaddamar da bincike, bayan wasu rahotanni sun ce an gano burbushin sinadarin Polonium mai yawa a jikinsa kayyakinsa.

Isra'ila dai ta musanta cewa tana da hannu a mutuwarsa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.