BBC navigation

Kano: 'yan fashi sun kai hari a WAPA

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:23 GMT

'Yan sandan Najeriya

Rahotanni da ke Kano a arewacin Najeriya na cewa, wasu da ake zargin 'yan fashi ne sun kai hari a kasuwar canjin kuɗaɗe ta WAPA inda suka kashe mutum guda, kana suka yi awon gaba da kuɗaɗen da ba a kai ga tantance yawansu ba.

Kasuwar musanyen kudaden ta WAPA dai ta sha fuskantar hare-hare irin wannan a baya, kuma a wannan karon 'yan fashin sun dirar musu ne da rana tsaka.

A nata ɓangaren, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta samu labarin aukuwar lamarin, kamar yadda kakakinta ASP Mustapha Abubakar ya shaida min ta wayar tarho.

Kakakin rundunar 'yan sanda ta Kano ya ce sai nan gaba ne za su yi ƙarin bayani kan irin ɓarnar da aka yi a lokacin harin.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.