BBC navigation

Ana ƙidayar 'yan gudun hijira Mali dake Nijar

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:30 GMT

A jamhuriyar Niger yau ne hukumomin kasar tare da hadin gwiwar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya UNHCR suka soma wani shirin yin rajistar 'yan gudun hijiran kasar Mali da ke zaune a cikin kasar.

Wannan rejistar wacce ita ce ta biyu za ta baiwa hukumomin na Niger da ma sauran masu tallafa ma 'yan gudun hijiran damar sanin hakikanin adadinsu, da wuraren da suke zaune ta yadda za'a san bukatunsu ta fuskar abinci, da magunguna.

Kimanin 'yan kasar Mali dudu sittin da daya ne ke zaman gudun hijira a Niger yanzu haka sakamakon tashin hankalin da kasarsu ta fada.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.