BBC navigation

Najeriya: za'a zartar da tsarin 'kamun kafa'

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:17 GMT

Aminu Tambuwal, kakakin majalisar wakilan Najeriya

Majalisar dokokin Najeriya ta ce tana duba yiwuwar zartar da dokar shigar da tsarin kamun kafa a tafiyar da siyasar ƙasar.

Batun kamun kafa a harkokin majalisun dokoki wanda a turance ake kira 'Lobby' batu ne da ya samu karbuwa a tsarin tafiyar da harkokin majalisun dokokin wasu kasashen da suka ci gaba.

Ana dai amfani da wannan tsari ne wajen biyan bukatun wasu mutane da ma manyan kamfanoni.

Tsarin na kamun ƙafa dai ana amfani da shi ne wajen yin tasiri akan dokokin gwamnati.

Sai dai kuma koda a Amurka inda wannan tsari ya samu karɓuwa ana ta cece-kuce akansa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.