BBC navigation

Ana binciken manyan hafsoshin sojin Amurka

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:54 GMT
Shugaba Obama, Petraeus da wasu jami'an Amurka

Shugaba Obama, Petraeus da wasu jami'an Amurka

Shugaba Obama ya dakatar da mika sunan Babban Hafsan sojan Amurka a Afghanistan, Janar John Allen, don ya zama Babban kwamandan sojojin kungiyar kawancen tsaro ta NATO.

George Little kakakin ma'aikatar tsaron Amurka ya ce Sakataren tsaro ya gabatar da wannan bukata ga shugaban kasa, kuma shugaban ya amince ya dakatar da wannan nadi har sai an kammala bincike.

Ma'aikatar tsaron dai na bincike ne kan zargin da aka yi cewa Janar Allen ya tura wasu sakonni da ba su dace ba zuwa wata mata dake da hannu a abun kunyar nan da ya kai ga murabis din datsohon Direktan Kungiyar leken asirin Amurka, CIA, David Petraeus.

Janar Allen dai wanda ya musanta cewa ya yi ba daidai ba, ana binciken sa ne game da musayar dubban sakonnin email da ake zargin ya yi da Jill Kelley.

Ita ma Ms Kelly din ta ce ta samu sakonnin email da ke yin barazana ga rayuwarta daga maatar da David Petraeus ya yi fasinkanci da ita.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.