BBC navigation

Kawancen 'yan adawar Syria ya samu karbuwa

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:39 GMT

Taron ministocin harkokin wajen kasashen larabawa

Kungiyar Hadin kan kasashen Larabawa, Arab League, ta yi marhabin da kafa sabuwar hadakar kungiyoyin adawar Syria, sannan tayi kira ga dukkanin kungiyoyin da ke adawa da gwamnatin Syrian da su shiga wannan Kungiyar.

A wajen wani taron da tayi a birnin Alkahira ranar litinin kungiyar ta ce ta hakan za a amince da hadakar a matsayin halattacciyar wakiliyar al'ummar Syria.

Sai dai kuma ministocin Kungiyar Kasashen Larabawan da suke taron a Alkahira ba su fito fili suka fayyace ko a wurinsu kungiyar hadakar ita ce kadai halattacciyar muryar al'ummar Syria ba.

Bayan taron Firayin Ministan Qatar Sheik Hamad Bin Jassim ya yi wa 'yan jarida jawabi inda ya ce majalisar ministocin kungiyar kasashen Larabawa ta godewa Qatar saboda cimma yarjejeniyar aka yi a Doha da ta kafa sabuwar majalisar hadakar ta 'yan adawar Syria, ta kuma bukaci sauran 'yan adawa da su shiga cikinta.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.