BBC navigation

Jam'iyyar Communist ta China ta kammala taronta

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:42 GMT

Shugaba Hu Jintao tare da mataimakinsa Xi Jinping a wajen taron jam'iyyar ta Communist

Jam'iyyar Communist Party ta kasar China ta kammala babban taronta karo na 18 a birnin Beijin, kwana daya kafin a bayyana sunayen sababbin shugabannin da za su mulki kasar cikin shekaru goma masu zuwa.

Shugaban kasar na yanzu Hu Jintao zai sauka daga zama shugaban jam'iyyar inda mataimakinsa Xi Jinping wanda ya nada a zaman wanda zai gaje shi, zai maye gurbinsa.

Jam'iyyar ta kammala taron na tsawon mako daya ne da zabar wakilan kwamitin da 'ya 'yansa ne za su kasance sababbin shugabannin kasar.

Fiye da delegate-delegate 2,200 na jam'iyyar ne suka zabi sababbin wakillan babban kwamitin gudanarwa na jam'iyyar , yayinda su kuma wakilan wannan kwamitin suka nada kwamitin koli na dindindin wato Politburo wanda shi ne ke zaman majalisar zartarwar kasar.

Bayyana sabbin shugabanni

A ranar Alhamis ne dai za a bayyana jerin sunaye wakilan kwamitin na Politburo- wadanda sune shugannin kasar har nan da shekaru 10 masu zuwa.

A wajen taron dai an nada mataimakin shugaban kasar na yanzu Xi Jinping a zaman shugaban Jam'iyyar kuma ana sa ran shi ne zai karbi ragwamar shugabancin kasar daga Hu Jintao a watan Maris mai zuwa.

Kasar ta China dai kan sauya shugabanni ne bayan kowadanne shekaru 10 a wajen babban taron jam'iyyar ta China Communist Party irin wannan da aka kammala ranar Laraba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.