BBC navigation

Wani matashi a Nijar ya ƙirƙiro jirgin sama da bai buƙatar matuƙi

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:34 GMT
Jirgin sama

A jamhuriyar Nijar wani matashi mai suna Abdul’aziz Kunce, ɗan shekara 28, ya ƙirƙiro wani ɗan ƙaramin jirgi da bai buƙatar matuƙi.

Karo na farko ke nan da wani ɗan Nijar ya ƙirƙiro da irin wannan jirgin.

Jirgin da ya ƙeran dai yana iya tashi tsawon minti arba’in da biyar a sama tare da cin kilomita gommai.

Za a iya amfani da jirgin saman wajen ɗaukar hotuna da sauran bayanai daga sama.

Abdul’aziz Kunce dai, jika ne ga tsohon shugaban ƙasar ta Nijar, Janar Seyni Kountche, wanda ya yi mulkin soja daga 1974 zuwa 1987.

Abdul’aziz dai ya jima yana sha’awarar ƙere-ƙeren jiragen sama.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.