BBC navigation

An kashe jagoran Kungiyar Hamas a Gaza

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 18:39 GMT
Ahmed Jabari

An hallaka jagoran kungiyar Hamas

An kashe kwamandan dakarun kungiyar 'yan gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas, Ahmed Jabari, a wani harin da Isra'ila ta kai ta sama a kan motarsa a Gaza.

Ahmed Jabari shi ne wani kusa a kungiyar Hamas da aka kashe tun bayan da Isra'ila ta fara kai hare hare a birnin shekaru hudun da su ka wuce.

Har yau wani da ake tsamannin mataimakinsa ne ya rasa ransa.

Kungiyar Palasdinawa ta Hamas din ta ce harin da Isra'ilan ta kai ya bude wutar rikici kenan.

Mai magana da yawun Hamas din Taher al- Nounou ya ce baza su mika wuya ba, za kuma su ci gaba da gwagwarmaya da Isra'ila.

A na dai ta jin karar aman bindiga a zagayen birnin Gazan yayin da ake yada labarin kisan a masallatai,kuma an samu rudani a asibitin da da akai kai Ahmed Jabarin.

Israi'ila ta dau alhakin kisan

Isra'ila ta ce ta kashe kwamandan dakarun kungiyar Hamas din ne sabilida rawar da ya taka a kusan shekaru 10 da aka kwashe ana ta'addanci a yankin

Ta kuma ce wani martani ne ga makaman rokar da Paladinu ke ta harba wa kudancin Isra'ila a makwannin baya-bayanan.

Waklin BBC ya ce dama an yi tsammanin irin wannan ya faru bayan da a karshen makon da ya wuce 'yan gwagwarmaya su ka harba daruruwan rokoki cikin Isra'ila daga Gaza.

Dakarun sojin Isra'ila sun ce kisan Ahmed Jabarin ya bude hanyar karin kai hare hare kan kungiyoyin 'yan gwagwarmaya a Gaza.

Yanzu haka ta kai hare hare a kusan wurare 20 a Gaza kuma ta na kai hare haran ne da nufin lalata wuraran harba makaman roka na Hamas da kungiyar masu fafutuka ta Islamic Jihad.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.