BBC navigation

Olusola Saraki ya rasu

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 08:58 GMT
Nigeria

Shahararren dan siyasar nan na jihar Kwara da ke tsakiyar Najeriya Dr Olusola Saraki ya rasu.

Saraki wanda shi ne jagoran masu rinjaye a majalisar dattijan Najeriya a zamanin jamhuriyya ta biyu, ya rasu ne yana da shekaru 79.

Wata majiya a fadar gwamnatin jihar Kwaran ce ta tabbatar wa da BBC mutuwar tasa.

Majiyar ta kuma ce a ranar Larabar nan ake sa ran za a wuce da gawar sa daga Lagos zuwa Kwara domin yi masa jana'iza.

Saraki wanda ya rike sarautar gargajiya ta wazirin Ilori shi ne mahaifin tsohon gwamnan jihar Kwara Bukola Saraki wanda a yanzu dan majalisar dattijai ne.

Marigayin ya zamanto mafi fada a ji a siyasar jihar Kwara a tsawon shekaru da dama da suka gabata.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.