BBC navigation

Laraba ce ranar yaki da cutar Sukari

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 09:03 GMT

Gwajin cutar ciwon sukari

Ranar Larabar 14 ga watan Nuwanba ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin bukin yaki da cutar Sukari wato Diabetes a duniya a wannan shekara.

Hukumar lafiya ta duniya ta kebe wannan rana ce da nufin fadakar da jama'a irin illolin dake tattare da cutar da kuma hanyoyin kaucewa kamuwa da ita.

A cewar hukumar, kimanin mutane miliyan 346 a fadin duniya suka kamu da cutar ya zuwa yanzu , kuma wannan adadin a cewarta, ka iya nunkawa nan da shekarar 2030.

Masana kiwon lafiya sun ce gadon kwayar cutar, da yawan cin abinci mai sanya kiba da kuma rashin motsa jiki sune ke kan gaba wajen bazuwar cutar a tsakanin mutane a yanzu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.