BBC navigation

Ambaliyar Ruwa: IRC ta ziyarci Najeriya

An sabunta: 15 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 08:51 GMT

Ambaliyar ruwa ta raba dubban mutane da muhallansu a Najeriya a tsakiyyar wannan shekarar

A Najeriya, yanzu haka wata kungiyar bada agaji ta kasa da kasa wato International Rescue Emergency, IRC, daga Burtaniya, ta soma wata ziyara a yankin tsakiyar kasar.

Kungiyar na gudanar da ziyarar ce domin ganewa idonta irin barnar da ambaliyar ruwa ta haddasa a daminar bana a wasu sassan kasar.

Jam'iar kungiyar mai kula da muhalli da kiwon lafiya Bobi Morris, ta shaidawa BBC cewar suna gudanar rangadi ne na yankunan ambaliya ta yiwa barna, kuma ya zuwa yanzu sun ziyarci mutane kusa 130,000 da ambaliyar ta shafa wadanda ta ce suna fuskantar karancin abinci.

Ambaliyar ruwan da ta afku a wannan shekarar a Najeriya dai ita ce mafi muni a cikin shekaru 50.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.