BBC navigation

Israila za ta fadada hare-hare kan Gaza

An sabunta: 15 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 08:01 GMT

Falasdinawa sun taru a wajen da sojan Israila suka hallaka Shugaban reshen sojin na Hamas, Ahmed Jabari.

Farayin Ministan Israila Benyamin Natanyahu yace kasar a shirye take fadada hare-haren da ta fara kaiwa mayakan kungiyar Hamas a yankin zirin Gaza.

A jawabinsa na farko tun bayan kashe shugaban bangaren soji na kungiyar Hamas Ahmed Jabari, Mr. Natanyahu yace Israila ba za ta dauki cigaba da kaiwa 'yan kasar ta hare-haren rokoki da sauki ba.

Israilan ta ce tuni ta riga ta kaiwa cibiyoyin sojin Hamas guda ashirin da ke sassa daban-daban na Gaza hari, amma majiyoyin asibiti a yankin sun ce an kashe akalla fararen hulla goma da suka hada yara da dama.

Amma a cikin daren da yayi kalaman, mayakan Palasdinawa suka fara mayarda martani da harba rokoki kan garuruwan da ke kudancin Israila.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.