BBC navigation

Shugabanin Nijar da Faransa na ganawa a Paris

An sabunta: 15 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 08:34 GMT

Shugaban Jamhuriyar Nijar Muhammadou Issofou

Shugaba Mahamoudou Issoufou na Jamhuriyar Nijar na ganawa da takwaransa na Faransa Francois Hollande yau Alhamis birnin Paris.

Tun a ranar Litinin ne dai shugaban na Nijar ya isa birnin na Paris, inda ya gana da masu zuba jari daga kasashen waje dake a Faransar, a wani yunkuri na bunkasa tattalin arzikin kasarsa.

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar ta Nijar Malam Bazoum Muhammed, wanda kuma ke cikin tawagar shugaban kasar, ya shaidawa BBC cewa batun warware rikicin kasar Mali na daga cikin abubuwan da shugabanin biyu zasu tattauna akai.

Jamhuriyar Nijar dai na daga cikin kasashen yammacin Afrika uku da suka yi tayin bayarda gudummuwar soji mafi girma inda za'a dauki matakin soiji kan 'yan tawaye a arewacin kasar Mali.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.