BBC navigation

A karon farko JTF ta kai hari ta sama a Maiduguri

An sabunta: 16 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:07 GMT
Jami'an tsaro a Najeriya

Jami'an tsaro a Najeriya

Rahotanni daga Maidugurin jihar Borno a arewacin Najeriya na cewa wasu mazauna wasu unguwanni a birnin sun kaurace wa unguwanninsu sakamakon samamen da jami'an tsaron hadin gwuiwa suka kai a unguwannin.

Rundunar tsaro ta JTF ta ce ta kai samamen ne da hadin gwuiwar sojojin sama na rundunar tsaro ta farin kaya da kuma tankokin yaki, inda ta ce ta samu nasarar kashe wani da ta ce babban kwamandan kungiyar Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati Waljihad ne da aka fi sani da Boko haram.

JTF ta ce shi ne ake zargi da hannu a kashe Janar Mamman shuwa.

Rundunar sojin ta Najeriya ta ce mutumin da ta kashe shi ne ya bayar da umarnin kisan wani tsohon janar na soja da aka yi kwanan nan wato Janar mamman Shuwa mai ritaya.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce mutumin da suka kashe mai suna Ibn Saleh Ibrahim babban kwamandan kungiyar Boko Haram ne a yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabas.

Wasu mazauna yankunan da abin ya faru sun yi min karin bayanin yadda samamen ya auku:

Shi ma wannan mazaunin unguwar ya ce sojojin sun yi amfani da jiragen sama a lokacin samamen:

Sanarwar rundunar sojin Najeriya ta ce rundunar za ta ci gaba da kai hari, kuma tuni ta samu nasarar gano wadansu makamai da abubuwa masu fashewa.

Kakakin Rundunar Tsaron ta Hadin Gwiwa mai aikin tabbatar da tsaro a Jihar Borno, Laftanar Kanar Sagir Musa, ya tabbatar da cewa sun yi amfani da jirage masu saukar ungulu da motoci masu sulke wajen kai harin.

Sai dai kuma ya ce bai san adadin mutanen da aka kashe yayin harin ba.

A lokuta da dama sojojin Najeriya kan bayyana irin nasarar da suka samu wajen yaki da wadanda suka kira 'yan ta'adda, amma ana zargin suna boye adadin sojojinsu da aka kashe ko kuma fararen hular da suka rasa rayukansu a hare-haren zargin da sojojin ke musanta wa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.