BBC navigation

Najeriya za ta tura soji Arewacin Mali

An sabunta: 16 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:27 GMT
Ola Ibrahim

Babban Hafsan Dakarun Tsaron Najeriya, Admiral Ola Ibrahim

Najeriya na sa ran cikin wasu 'yan makwanni masu zuwa za ta tura sojojn ta zuwa arewacin Mali da nufin yakar 'yan kishin Islamar da suka kwaci iko da mulkin yankin.

Babban hafsa na sojojin Najeriyar Admiral Ola Ibrahim ya shaidawa BBC cewa Najeriyar za ta ba da kimanin sojoji dubu daya cikin sojoji fiye da dubu ukun da kungiyar raya tattalin arzikin yankin ke bukatar turawa a can.

Admiral Ibrahim yace, "a duk lokacin da aka samu matsala a yankin Afrika ta yamma, a shirye suke su bayar da goyon bayan da za su iya bayarwa wanda Shugabannin gwamnatocin kasashen yankin ke bukata.

A yau Jumma'a, Shugaba Blaise Campore na Burkina Faso zai gana da kungiyar 'yan kishin Islama ta Ansarud Deen da ta Abzinawa a wani bangare na kokarin neman maslaha ga rikicin kasar ta Mali.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.