BBC navigation

Isra'ila ta amince da kiran soji 75,000

An sabunta: 17 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 05:56 GMT

Hedikwatar Hamas da Israila ta kaiwa hari

Isra'ila ta amince a kira sojojin da aka baiwa horo na wucin-gadi kimanin dubu saba'in da biyar a yayin da take ci gaba da kai hari ta sama a kan Hamas da sauran mayaka a zirin Gaza.

Kiran sojojin zai kara tabbatar da rade-radin da ake yi cewa Isra'ilar tana shirin mamayar Gaza ne ta amfani da mayakan kasa.

Tun farko a ranar Juma'a, a karon farko mayakan Palasdinawa sun harba makamin roka a yankin birnin Kudus, haka kuma sun harba wani zuwa yankin birnin Tel Azviv.

Isra'ilar dai ta killace manyan hanyoyin dake kewayen Gaza tare da shelar yankin a matsayin yankin da sojoji suka hana shiga.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.