BBC navigation

Isra'ila ta ce zata cigaba da kai hare-hare akan Gaza

An sabunta: 17 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:54 GMT

Yayin da aka shiga rana ta hudu a hare-haren da Isra'ila tace zata cigaba da ka hari akan yankin Gaza inda kungiyar Hamas iko.

Isra'ilan ta kuma ce, ta lalata wuraren ajiye rokoki na karkashin kasa na Palasdinawa.

Ministan hulda da kasashen waje na Tunisia, Rafik Abdessalem, wanda yake ziyara a yankin na Gaza, yayi kira ga shugabannin kasashen larabawa su kawo karshen abinda ya kira, wuce gona da iri da Isra'ila take yi.

Ministan yace, abinda Isra'ila take yi a yankin Gaza ba za'a lamunta ba, abu ne da bai halasta ba. Kuma ya kamata Isra'ila ta sani cewa, duniya fa yanzu duniya ta sauya.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.