BBC navigation

A Jordan anyi arangama tsakanin masu bore da masu marawa gwamnati baya

An sabunta: 17 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:03 GMT

zanga-zanga a Jordan

A kasar Jordan an yi arangama tsakanin masu bore dake adawa da gwamnatin kasar da magoya bayan Sarki Abdullah.

An fara dauki ba dadin ne bayan wata zanga-zanga da dubban mutane suka yi a Amman babban birnin kasar saboda karin kudin mai da gwamnati ta yi a farkon mako.

Wasu masu boren sun rinka kwakwazo suna kiran Allah Ya karya gwamnatin Sarki Abdullah, abinda kusan za a ce bai taba faruwa ba a kasar Jordan, yayin da wasu masu biyayya ga Sarkin, suka fantsama kan tituna don nuna goyon bayan su gare shi.

Suna cewa "Wannan kasar mu ce Jordan, kuma za mu iya sadaukar da rayukan mu saboda Abu Hussain.

Tun lokacin da aka yi karin kudin man, farashin iskar gas ya haye da kashi hamsin bisa dari, yayin da farashin man diesel da Kananzir su ma suka hau-hawa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.