BBC navigation

A Mali fada ya barke tsakanin 'yan tawaye da masu Kishin Islama

An sabunta: 17 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:22 GMT

Masu kishin Islama a Mali

Fada ya barke tsakanin 'yan tawaye na Abzinawa da mayaka 'yan kishin Islama a yankin arewacin Mali.

Kungiyar Abzinawa MNLA ta ce tana kokarin fatattakar 'yan kishin Islama din ne daga garin Gao.

Kungiyoyin suna hada kai da juna tun lokacin da suka kwaci iko da mulkin yankin a farkon wannan shekarar, to amma sun samu sabani a kan ko za su shiga tattaunawar sulhu da gwamnati a Bamako.

Sun kaure da fadan ne a daidai lokacin da Kungiyar kasashen Yammacin Afrika ke kammala shirye-shirye na tura dakarun da za su yaki 'yan tawayen a yankin arewacin kasar ta Mali.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.