BBC navigation

An kammala zabe a Saliyo

An sabunta: 17 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:05 GMT

An kawo karshen kada kuri'a a zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki a kasar Saliyo. Ba dai wani rahoton aukuwar tashin hankali, kuma bisa ga dukkan alamu jama'a da dama sun fito sun kada kuri'a.

An samu gagarumar fitowar jama'a a rufunan zabe a ksar Saliyo inda ake zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki.

Masu kada kuri'a sun yi cocirundo a rumfunan zabe da aka kafa a cikin makarantu da wasu gine-ginen gwamnati a babban birnin kasar Freetown.

Shi dai shugaba mai ci, Ernest Bai Koroma yana neman wa'adin mulki na biyu ne a fafatawa mai zafi tsakaninsa da babban abokin karawarsa, Julius Maada Bio.

Dubban 'yan kasar ta Saliyo ne ke sa ido akan wannan zabe, kuma gwamnatin Birtaniya ne ce ta bada tallafin biyansu domin yin wannan aiki.

Ana dai kallon wannan zabe a matsayin wata alamar farfadowar kasar ta Saliyo daga mummunan yakin basasar da ta fuskanta.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.