BBC navigation

Harin Isra'ila ya kashe kananan yara

An sabunta: 18 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 05:17 GMT

Jaririn da aka kashe a harin da Israila ta kai Gaza

Isra'ila ta cigaba da ruwan bama-bamai kan Gaza a daren jiya yayin da take amfani da jiragen sama da kuma hare-haren jiragen ruwan ta na yaki.

Jami'an kiwon lafiya na Palasdinawa sun ce wani harin da Isra'ilar ta kai ya hallaka wasu jarirai biyu 'yan gida daya.

Wani bam din kuma da ya fada kan wani gini da 'yan jarida na cikin gida ke cikinsa ya jikkata 'yan jarida shida.

Wani wakilin BBC a birnin Gaza ya ce kusan babu kowa a titunan birnin a yayin da manya da kananan jiragen yaki na Isra'ila ke kai hare -hare.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce asibitoci a Gaza sun cika makil da wadanda suka samu raunuka magunguna kuma sun yi karanci.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.