BBC navigation

Shevchenko ya ki karbar mukamin koci

An sabunta: 19 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:09 GMT

Andriy Shevchenko

Andriy Shevchenko ya ki amincewa da damar da kasar Ukraine ta ba shi don kasancewa sabon kocinta, yana mai cewa bai shirya karbar aikin ba.

Hukumar kwallon kafar kasar ta shiga kasuwa don neman sabon koci ne bayan kocinta, Oleg Blokhin, ya koma kungiyar Dynamo Kiev a farkon kakar wasanni ta bana; kuma tuni ta yanke shawarar cewa tsohon dan wasan AC Milan din ne ya dace ya karbi mukamin.

Sai dai Shevchenko, mai shekaru 36, ya ce lokaci bai yi ba da zai jagoranci babbar kungiyar kwallon kafa ta kasa.

Ya ce: "Ina ganin ban yi kwarin da zan shugabanci babbar kungiyar kwallon kafar Ukraine a halin da ake ciki ba. Ina fata shagabannin hukumar kwallon kafar kasar za su fahimci dalilai na''.

Ukraine ce ta biyar a rukunin H na wasan cancantar shiga Gasar cin Kofin Duniya ta shekarar 2014, inda suka samu maki biyu a wasanni uku da suka buga.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.