BBC navigation

Rikici ya sake barkewa a Ibbi

An sabunta: 19 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:48 GMT

Rikici ya sake barkewa a garin Ibbi na jihar Taraba da ke arewa-maso-gabashin Najeriya da safiyar yau din nan, inda a kalla mutum biyu suka rasa rayukansu.

Wasu mazauna garin na zargin cewa wasu mayakan haya ne suka far ma garin a kokarin kai wa 'yan uwansu dauki, duk kuwa da dokar hana fitar da gwamnatin jihar ta sanya.

A jiya ne dai rikici mai kama da na addini ya barke a garin tsakanin wasu mabiya addinin kirista da ke ibadar Lahadi bayan sun datse wata hanyar da ke kusa da majami'arsu.

Bayanan da ke fitowa daga garin na Ibbi na nuna cewa rikicin na nema ya rikide daga na addini zuwa na kabilanci, sakamakon wani sabon harin da wasu da mazauna garin ke zargin cewa baki ne suka kai kan kabilar Hausawa da sauran dangoginsu da ke garin.

Mazauna garin dai sun ce baya ga asarar dukiya an yi asarar rayuka saboda an kashe a kalla mutum, amma kawo lokacin da nake hada wannan rahoton ba a tabbatar da wannan lamari a hukumance ba.

A jiya ne dai aka samu tashin hankali a garin na Ibbi bayan wasu mabiya addinin kirista sun toshe wata hanya da ke kusa da majami'arsu da ke unguwar Mallam Gambo domin su samu zarafin bautar ubangiji, inda al'umar musulmin da ke kewayen suka nemi sai sun bi hanyar saboda a cewarsu ita ce kadai hanyar zirga-zirga a unguwar.

Kuma daga nan suka hau dokin-zuciya har aka kai ga rasa rayuka da kone-konen gidaje.

Tun a jiyan dai gwamnatin Jihar Taraban ta sanar da dokar hana fita a garin, tare da kai jami'an tsaro domin wanzar da zaman lafiya.

Idan har zargin cewa mayakan haya ne suka kai ya tabbata, to abin tambaya shi ko a ina jami'an tsaro suke har maharan suka kutsa suka yi aika-aikar tasu?

Rayuwar a garin na Ibbi kamar yadda mazaunansa ke cewa ta yi wuya.

Duk kokarin BBC na ji daga shugabannin kabilun yankin dangane da zargin cewa rikicin na neman narkewa zuwa na kabilanci ya ci tura. Kazalika shi ma kwamishinan 'yan sandan jihar bai samu ta waya ba.

Sai dai Sarkin Ibbi Alhaji Abubakar salihu Danbawo ya ce gwamnati ta dauki matakan shawo kan rikicin, saboda an tanadi jami'an tsaro, haka kuma ana kokarin zama da shugabannin addini da na kabilun yankin don samun maslaha.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.