BBC navigation

Barack Obama zai fara ziyara zuwa Burma

An sabunta: 19 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 05:49 GMT

Barack Obama

Shugaba Obama zai fara wata ziyara mai dimbin tarihi a Burma - ziyarar farko da wani Shugaban Amurka mai ci ya taba kaiwa a kasar.

Ziyarar na nufin nuna goyon baya ga shirin gyare-gyaren siyasa da Shugaba Thein Sien ke aiwatar wa.

Kafin isar sa Burman, Shugaba Obama ya ce ba wai yana son nuna amincewa da gwamnatin Burma ba ne, yana son ya nuna gamsuwa ne da sauye-sayen demokradiyyar da ake samu a can, wadanda babu wanda ya yi tsammani za a taba samu a wannan lokacin.

A ran jajiberin ziyarar ta sa, gwamnatin Burma ta sanar da yin afuwa ga karin wasu fursunoni sittin da shida wadanda suka hada da wasu sanannun 'yan siyasa dake tsare.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.