BBC navigation

Hadduran mota na hallaka rayuka a Najeriya

An sabunta: 19 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:27 GMT

A najeriya, mutune sama da ashirin ne ciki har da kananan yara shida suka rasu a wasu munanan haduran mota biyu da suka abku a kan hanyar Talata Mafara zuwa Gusau da kuma kwanar-Kalgo da ke jihar Zamfara.

Haduran dai sun faru ne sakamakon taho mu gamar da aka yi tsakanin wata motar Golf da ta fito daga Gusau zuwa Sokoto da wata motar safa mai kirar Haice, yayin da wata motar safa kuma ta saki hanya.

Daya daga cikin haduran dai, kamar yadda Kwamandan hukumar kiyaye hadura ta jihar Zamfara, Abdulkadir Bala Mohammed ya bayyana ya auku ne tun da safiyar yau bayan wata mota mai dauke da 'yan buki mata kimanin mutum goma sha bakwai ta tashi daga Abuja ta saki hanya a Kwanar Kalgo a kan hanyarta ta zuwa Sokoto, yayin da daya hadarin kuma ya ritsa da motoci da suka yi taho mu gama, motocin da jami'in ya ce an musu kazamin lodi, kasancewar an loda muta ne har a but.

Wannan hanya ta Talatan Mafara zuwa Sokoto da wasu hanyoyin da ke yankin sun yi kaurin -suna wajen haddasa haduran da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama sakamakon rashin kyawonsu.

Sai dai Kwamandan ya ce, a fahintarsu haduran na wannan karon na da nasaba da sakacin matuka.

Ita ma kungiyar Direbobin Najeriya a nata bangaren ta ce da wuya a samu matukanta da matsalar tukin ganganci ko gudun sauri-ba-wurin-zuwa, kuma kungiyar ba ta bari a yi lodi fiye da kima.

Hadarin mota a Najeriya dai, kamar yadda hukumomin da abin ya shafa ke fitar da alkaluma na cewa yana cin rayukan jama'a fiye da illar da cutar sida ke yi.

Duk da cewa kowane bangare na kokarin fita daga laifi, kwararru na ganin cewa lalacewar hanyoyi, da tukin ganganci na daga cikin abubuwan da ke haddasa hadarin mota a kasar, yayin da a bangare guda kuma wasu ke zargin mahukunta da laifin ba da lasisin tuki ga 'yan kasar da dama ba tare da yin gwaji ba saboda gata ko dan abin hasafin da suke bayarwa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.