BBC navigation

Isra'ila da Hamas sun tsagaita wuta

An sabunta: 21 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 18:34 GMT
Isra'ila da Hamas sun tsagaita wuta

An kashe akalla mutane 160 mafiya yawansu Falasdinawa

Israel da kungiyar Hamas mai mulkin yankin Falasdinawa na Gaza, sun amince da yarjejeniyar tsagaita wutar da ta kawo karshen tashin hankalin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 160 mafiya yawansu Falasdinawa.

Ana saran za ta fara aiki ne da misalin karfe 7.00 agogon GMT wato karfe 9.00 agogon yankin, a cewar jami'an Masar da suka shiga tsakani.

An dai samu tsaiko wurin cimma makamanciyar wannan yarjejeniyar a ranar Talata.

Kimanin mutane 13 ne suka mutu a ranar Laraba a ci gaba da luguden wutar da Isra'ila ke ye a zirin Gaza.

Yayin da wani bam ya tashi a wata motar Bus a birnin Tel Aviv na Isra'ila, inda mutane da dama suka samu raunuka.

Ministan harkokin wajen Masar Kamel Amr shi ne ya bayar da sanarwar tsagaita wutar a wani taron manema labarai tare da sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton a birnin Alkahira.

Kawo yanzu babu cikakken bayani kan sharudan da ke kumshe a cikin yarjejeniyar, a cewar editan BBC na yankin Gabas ta Tsakiya Jeremy Bowen.

Sai dai ana saran shugabannin Hamas da na kungiyar Islamic Jihad za su gabatar da jawabi nan gaba kadan, inda za su fayyace abinda yarjejeniyar ta kunsa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.