BBC navigation

Yunkurin diflomasiyya na sasanta Gaza da Isra'ila

An sabunta: 20 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:17 GMT

An zo wata gaba a rikicin da ake yi tsakanin Isra'ila da Hamas. Manyan aminan Isra'ila, wato Amurka da nahiyar Turai, wadanda ke zargin Hamas da tayar da rikicin, sun baiwa Isra'ila wata dama ta tsagaita kai hare-hare, sai dai da alama wannan damar na neman kubuce wa.

Idan Isra'ila ta ci gaba da kai hare-harenta ta sama, hakan zai sa a kara samun mutuwar mutane da dama, abin da kuma ka iya janyo wa Isra'ilan rasa goyon bayan diflomasiyyar da take samu.

An shafe karshen makon da ya gabata ana kokarin diflomasiyya tsakanin kasashen Masar da Turkiyya da kuma Qatar da nufin samo hanyar kawo karshen rikicin, sai dai kuma hakan bai cimma wata kwakkwarar nasara ba, saboda Isra'ila na ci gaba da kai hare-haren ta inda ake kara samun rasa rayukan mutane da dama.

Sai dai dukkan bangarorin za su so a tsagaita wuta, don gudun kada Isra'ila ta kai hari ta kasa a Gaza.

Ana dai ci gaba da kokarin diflomasiyya ka'in-da-na'in domin tabbatar da tsagaita wuta, yayin da jami'an gwamnatin Isra'ila ke cewa ya kamata a samu wata mafita daga nan zuwa ranar Alhamis.

A hakikanin gaskiya, babu wani karsashi a Isra'ila na kai hari ta kasa a Gaza, amma idan har ba a sasanta ba, kasar ta Isra'ila za ta iya kutsawa da sojojinta wadanda tuni suke cikin shirin ko-ta-kwana.

Sai dai kuma duk wani yunkurin sasanta rikicin da za a yi, zai kasance ta bayan fage ne, saboda dukkanin bangarorin biyu, wato Isra'ila da Hamas, ba za su zauna teburin sulhu ba balle su sanya hannu a kan takardar yarjejeniyar tsagaita wuta.

Kowannen su na son nuna wata bajinta a karshen wannan rikicin.

Daya daga cikin dalilan da suka sa aka gaza cimma nasara a sasantawar diflomasiyya shi ne samun gagarumin sauyi a tsarin diflomasiyyar yankin Gabas ta Tsakiya.

Wani dalilin kuma shi ne rashin jituwa tsakanin Isra'ila da Turkiyya. Wani muhimmin batun shi ne sauyin gwamnati da aka samu a kasar Masar, gwamnatin da ake ganin tana goyon bayan Falasdinawa tana kuma kaffa-kaffa da Isra'ila.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.