BBC navigation

Isra'ila ta sake fadada hari kan Gaza

An sabunta: 20 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:34 GMT

Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare ta sama a Zirin Gaza kwana na bakwai a jere, yayinda su kuma Palasdinawa 'yan gwagwarmaya ke ci gaba da harba rokoki cikin Isra'ilar.

Jami'an kiwon lafiya a Gaza sun ce an kashe Palasdinawa 115 tun daga lokacin da Isra'ilar ta fara kai hare-haren bam ranar Larabar da ta wuce, yayinda aka kashe fararen hula 'yan Isra'ila ukku.

Jami'an kungiyar Hamas sun yi kira ga dakarunsu da su zafafa kai hare-hare a kan Isra'ila.

Rundunar sojan Isra'ila ta ce an harba rokoki akalla 90 ya zuwa yanzu a yau din nan.

Sai dai duk da hakan, a yanzu hankali ya karkata wajen bin hanyar diplomaisyya don neman tsagaita wuta.

Ana gudanar da wata tattaunawa a Alkahira, babban birnin kasar Masar.

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon shi ma ya je birnin na Alkahira yau inda ya yi kiran da a tsagaita bude wuta.

A yau din zai je Jerusalem domin ganawa da Piraministan Isra'ila, Benyamin Netanyahu, da sauran manyan jami'ai.

Ita ma Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, za ta isa wajen taron nan ba da jimawa ba.

Jami'an gwamnatin Masar sun ce akwai yiwuwar cewa za'a cimma yarjejeniya nan ba da dadewa ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.